Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hawan Idi


Gabatarwa

Hawa ne da sarki yake yi a ranar idi daga masallacin idi zuwa gidansa bayan an kammala dukkan abubuwan da suka dace na sallar idi. Ana yin wannan hawa a ranar idin Sallar Azumi da kuma Sallar Layya.

Sababben abu ne a gurin dukkan sarakunan Kano sukan tako da ƙafarsu daga gidansu zuwa masallacin idi domin ɗabbaƙa sunnar idi. Sannan kuma idan suka tashi komawa gida sai su canja hanya ita ma dai kamar yadda addini ya tanada. To a wajen wannan komawa gida, a nan ne sarki yake hawa doki tare da sauran mahaya da suka haɗa da dukkan sauran masu riƙe da muƙaman sarautar gargajiyar daga kan hakimai, dagatai masu unguwanni, bayi da sauransu.

Haka nan ma masu kaɗe-kaɗe da bushe-bushe suna yi ana tafiya ana karɓar gaisuwa da dandanzon mutanen da ke tsayawa jere a gefen hanya hagu da dama wasu a ƙasa wasu kuma a saman bishiyoyi, wasu a saman gidaje, wasu a saman ababen hawa, wasu na biye a ƙafa wasu kuma na biye a kan ababen hawa, masu kai komo suna yi. Abin sai wanda ya gani.

Wannan kuma shi ne yake zama mabuɗin bukukuwan salla a wannan gari na Kano da ma sauran garuruwan Ƙasar Hausa.

Sarki zai tashi daga filin idi, ya fita ta ƙofar Gabas, ya hau kan titin IBB a yanzu, a da kuma titin dogo; wato titin jirgin ƙasa, ya saka gabansa Arewa. Idan ya je ƙarshen masallaci daga Arewa, sai ya juya Yamma, ya tafi, sai ya je ƙarshen kasuwar Ƙofar Wambai sannan ya karyaka Arewa ya shiga Ƙofar Wambai, sai kuma sai ya tasa Kudu ya dawo ta Karofin Zage, ta jikin Asibitin Birni, ya shiga ta Shahuci, sannan ya isa Gidan Shatima gurin da tuni gwamna da sauran manyan baƙi suke dakon sarki. Idan ya je, sai sarki ya ja linzami ya tsaya sannan ya sauka su gaisa da gwamna da tawagarsa da kuma sauran manyan baƙi su yi wa juna barka da salla.

Bayan an gama da nan kuma sai sarki ya sake hawa sai Ƙofar Ƙwaru, inda zai je ya sauka. A nan kuma sai hakiman sarki su kai wa sarki Jafi. Ita kuwa jafi, salo ne na gaisuwa da hakimai da sauran masu riƙe da muƙaman sarauta suke zuwa ɗaya-bayan-ɗaya suna gai da sarki.

Bayan an kammala wannan gaisuwa da ake kira Jafi, sai kuma sarki ya yi wa Kanawa jawabi wanda yake a matsayin jawabin shekara-shekara. A nan kafafen yaɗa labarum da suke da wakilai a gurin za su je su naɗa su watsa a duniya. Daga nan kuma sai sarki ya shiga gida, sauran jama’a kuma kowa ya kama gabansa. Hawan Idi ya zo ƙarshe kenan.

Manazarta:


Gwangwazo (2004). Gamzaki mai Asubahi, In Ya fito Gari Ya Waye, Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub